Airdrop Hunting
Tabbas ana samun alkhairai sosai da airdrops, musamman airdrops na blockchains da wallets. Airdrop yana banbanta sosai da mining wajen yin tasks, a mafi yawan minings ina shiga ne duk bayan awa 24 ko wasu awanni ana yin claiming. Sabanin minings, mafi yawan airdrops tasks akeyi wayanda suka hada swaps, bridging, staking, providing liquidity, da sauransu.
Ba kamar minings ba (musamman na telegram) da ake kirkirarsu babu use case, mafi yawan projects da sukeyin airdrops sunada use cases dinsu. Wasu blockchains ne, wasu wallets ne, wasu lending protocols ne, wasu bridging platforms ne, wasu staking protocols ne, da sauransu. Don haka idan har zasuyi airdrops suna bada tasks wayanda suke da alaqa da use cases dinsu wanda mutane zasu dinga yi. Misali, idan blockchains ne kasancewa suna dauke da dukkan use cases da ka bukata a crypto, shine yasa zamuga tasks dinsu suna hada abubuwa da yawa, kamar swapping, bridging, staking, da sauransu. Kamar wallets, suna saka tasks na swapping, staking, providing liquidity da saurasu. Haka dai kowanne project da zasuyi airdrop, suna saka tasks daidai da use cases dinsu.
Projects da zasuyiairdrops (walau testnet, retroactive, da sauran rabe-raben airdrop) suna bada coins dinsu ne gwargwadon tasks da mutane sukayi. Misali, idan blockchains ne suna duba yawan transaction count da volume, don haka yawan kokarin mutum yawan abinda zai samu a airdrop. Muyi misali da Mango Network Airdrop da mukeyi, testnet airdrop ne amma sun kayyade adadin tasks da mutum zaiyi a rana na swapping, bridging, da sauran tasks wanda kullum sai mutum yayisu. Don haka wanda yake tsallake wasu tasks din daya yinsu, hakan zai taba rewards da zai samu. Amma mu dauki HAUST Network testnet airdrop da mukeyi, a yanzu iya swapping kawai akeyi a matsayin task, don haka wanda yafi yawan yin swapping (transaction count) shine zaifi yawan samun rewards.
A retroactive airdrops kuwa, suna kallon abubuwa kamar transaction count, volume, staking, da sauran tasks. Misali, mu dauki Base blockchain, har yanzu basuyi coin dinsu, don haka akwai kyakkyawan zaton suyi airdrop irin na Arbitrum blockchain. Ma'ana, su bawa wayanda suke transaction akan blockchain dinsu. Idan har zuasuyi hakan, to zasu kalli transaction count (adadin transaction da mutum yayi akan blockchain dinsu), sannan kuma zasu kalli volume na transactions dinsa (wato yawan kudin da yayi transactions dasu).
Shawarar dazan bamu itace, idan har zamuyi hunting airdrop to kada muyi masa yanda muke yiwa minings, ma'ana mu tara airdrops da yawa. A minings, zakaga mutum daya yana minings da yawa lokachi guda, kamar minings 20. A airdrops zaifi kyau mutum ya samu kadan masu kyau (gwargwadon lokachin da yake dashi) yana yinsu, ya rike musu wuta, yanayin duk wasu tasks dinsu, idan basu kayyade adadin transaction ba ya dage ya tara transactions count da volume, sannan ya bisu da addu'a. In Sha Allah sai kaga mutum ya samu rewards mai kyau adukkansu. Amma idan mutum ya tarawa kansa airdrops da yawa itin yanda muke yiwa mining, to karshe bazai jure yin tasks dinsu ba harya tara transaction count da volume. Idan anzo launching ace masa NOT ELIGIBLE, idan kuma yayi sa'a abashi rewards dan kadan yazo yana kunkuni.
Allah ya datar damu