Dukda cewa zanyi bayaninsu achikin bidiyon Dex, bari na danyi mana bayanin ma’anar wayannan crypto terminologies din.
✨ Rug Pull: Shine devs na token su rike kaso mai yawa na token din a wallet(s) dinsu, sai mutane da yawa sun saka kudinsu, sai devs din su sayarda dukkan token dake wallet(s) dinsu, wato dai suyi dumping. Hakan kuma sai yasa farashin token din yayi mummunar faduwa lokachi guda. İrin hakane zamuga lokachi guda farashin token yayi -90%. Misali farashin token yayi mummunan karyewa daga $1 zuwa $0.1 ko $0.001, hakan yake sawa mutum ya sayı token na $100 amma lokachi guda yaga ta koma $2 😭.
✨ Honey Pot: Shine devs suyi coding token dinsu akan cewa saidai a saya amma ba damar sayarwa. Nasan maybe kun taba samun hakan, wato kun sayi token amma kuma ba damar sayarwa. Wani lokachin zakuga kudin token din ya tashi sosai amma ba damar siyarwa. Ka sayi token na $100 ta koma $10,000 amma ba damar sayarwa, saidai kallo 😭.
✨Removing Liquidity: Shine ka sayi token, sannan zaka iya sayarwa amma lokachi guda kawai sai devs su zare masa liquidity. Hakan zaisa daga baya bazaka iya sayar dashi ba duk ribar daya ba, ya zama hoto kawai a wallet dinka. Bari muyi amfani da policy din tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari as case study. Nasan kun tun lokachin da Buhari ya ware tsofaffin kudaden N1000 da N500 akan cewa sun daina aiki, hakan na nufin ya zare musu liquidity 😃. Hakan na nufin abaya sunada daraja amma yanzu ba damar amfana dasu wajen siyayya.
✨ Shakeout: Strategy ne da project/token suke amfani dashi wajen korar paperhands. Paperhands ko kuma muce jeeters sune mutane da basa iya rike token na tsawon lokachi, wato da token yayi kasa kadan saisu sayar, ko kuma dazarar ya tashi saisu sayar. Paperhands suna mayarda project baya sosai, su hanashi motsin kirki. Don haka sai project su koresu ta hanyar yin amfani da shakeout strategy. Shakeout shine project suna dumping din token dinsu dagangan domin su kori paperhands. Misali, paperhands sun sayı token yanada $2M market cap (MC). Sai project su dinga dumping din token dinsu farashinsa yanayin kasa, MC tana yin kasa. Misali, suyi dumping project ahankali-ahankali, kamar daga $2M MC zuwa $1.8M MC, zuwa $1.5M MC, zuwa $1M MC. Kai zasu iyayin dumping har zuwa $500k MC domin su kori paperhands. Hikimar yin hakan shine sawa paperhands tsoro da fargaba a kowacce gaba ana korarsu. Misali, idan token ya koma $1.8M MC wasu daga chikin paperhands zasu sayar, wasu zasu sayar idan ya koma $1.5M MC. Haka dai abin zaichi gaba da kasancewa, token yana yin kasa paperhands suna sayarwa. Idan project suka gama yin kasa da token dinsu kuma saisu hanashi tashi kuma su hanashi sauka na tsawon lokachi, wato dai token din ya fara consolidation. Hakan zaisa sauran paperhands yan dagiya su sayar tunda farashin token ya tsaya waje daya. Sai rana daya kawai project suyi pumping token dinsu ya koma $2M MC dinsa, bayan sun tabbatar saura real holders na token dinsu.
Wannan karatune mai fadi da kuma muhimmanchi, zanyi mana bayaninsa a chikin bidiyon Dex da nakeyi. Musamman yanda mutum zai nemi tokens masu saukin MC da suke consolidation ya shiga domin holding.