Barka da Shigowa Sabuwar Shekara ta 2025
Dukkan yabo, godiya da kirari sun tabbata ga Ubangiji Allah (SWA), mahaliccin kowa da komai. Tsira da aminchin Allah su tabbata ga dan gatan Allah, chikamakin annabawa, shugaban manzanni Annabinmu Muhammad (SAW), da iyalan gidansa, da sahabbansa, da sauran salihan bayi da suka biyo bayansu da nagartattun ayyuka.
Hakika shakarar data gabata ta 2024 tazo da nasarori masu tarin yawa a wannan kasuwanchi namu na crypto dama tarayyarmu a kafafen sada zumunta da suka hada da Facebook, Telegram, YouTube da X, wato twitter. A 2024 Allah ya hadamu da masoya na gaske, masu yi mana fatan alkhairi da nasara a rayuwarmu, kuma tabbas munga tasirin addu'o'insu garemu. Na gode sosai da wannan soyayya da fatan alkhairi, UbangijiAllah yabar zumunchi, ya karfafemu baki daya, sannan ya nunka muku dukkan aminda kukeyi mini fata. Allah ya shaida nima ina kaunarku, kuma ina addu'ar Allah ya ninninka muku dukkan abinda kuke roka mini. Ubangiji Allah yasa albarkarsa a tarayyarmu.
Haka zalika a 2024 mun fuskanchi wasu qalubale kala-kala, saidai zuwansu ya karfafemu, tareda kara mana karfin tunani wajen magancesu. Mun fuskanchi kiyayya daga makiya da magauta. Muna addu'ar Allah ya karo mana yawan makiya, ya gajiyar dasu, ya karemu daga dukkan sharrinsu na fili dana boye, ya warware dukkan wani kulli da suke kullawa, Allah ya kiyayemu daga dariyar makiya. Allah ya tsaremu da tsarewarsa, ya bamu kariya daga gareshi.
Yau mun shigo sabuwar shekara ta 2025. Muna addu'ar Allah ya sadamu da dukkan alkhairan dake chikinta, ya tsaremu daga dukkan sharrukan dake chikinta, ya amintar damu. Allah ya tsaremu daga nunawa bayinsa kiyayya, mugunta, hassada, munafunchi, keta, zalunchi, da sauran munanan ayyukan daya hanemu dasu.
In Sha Allah yau zanyi mana bidiyo na shawarwari akan yanda zamu amfanar da kanmu a 2025 achikin kasuwanchinmu na cryptocurrency.