MULTI-SIG WALLET
Jiya nayi tambaya cewa mecece multi-sig wallet? Da kuma amfaninta. Mutane da yawa irinsu dan uwa Sheikh Barr. Abdul-Hadee Isah Ibraheem sunyi bayani daidai mai ma’ana akan mecece multi-sig wallet.
Atakaice dai multi-sig wallet kamar yanda sunan yake nunawa wallet cewa da mutum daya bashida iko da ita, bazai iya chire kudin dake chikinta kamar yanda zai yiwa personal wallet dinsa irinsu Metamask, Bitget wallet, Tonkeeper, OKX wallet, da sauransu. Multi-sig wallet mutane biyune zuwa sama suke haduwa budeta, ta yanda mutum daya bashida ikon chire dukiyar dake chikinta saida yarda wani kaso na adadin mutanen da suka budeta. Misali, mutane 10 şu hadu şu bude multi-sig wallet, tun farko saisu saitata cewa kudi bazai fita daga chikinta ba sai an samu yardar wani adadi daga chikin mutum goman nan sun amince/yarda (misali, mutane 7 achikin mutum goma). Don haka aduk lokachin da za’a chiri kudi a wallet din, zata turawa kowannensu notification, idan 7 sukayi confirming transaction din sai kudin şu fita. Mutane masu Multi-sig wallet suna aikine tamkar validators akan blockchain, ta yanda babu wani transaction da za’ayi akanta ba tareda yardar mafi rinjayensu ba.
Wani lokachi daya shude kamar shekara daya baya, şu Ismail Yahaya (ina tunanin sun haura su biyar) sun hada kudi domin yin farming din wani token na Wicrypt. Saida suka tara token din da yawa, na kudade masu nauyi, sai wani daga chikinsu da yake da access da wallet din ya debe dukkan tokens din basu sani ba. Saida sukayi dogon binchike a tsakaninsu sannan suka gano wanda ya kwashe tokens din. Inda ace sunyi amfani da Multi-sig wallet hakan bazai yiwuba.
Na dade ina hakaito amfanin Multi-sig wallet. Da ace mutane zasu rungumi amfani da ita, da za’a samu raguwar rigingimu tsakaninsu. Misali, mutanen da sukeyin adashe zasu iya amfani da multi-sig wallet, kungiyoyin al’umma zasu iya amfani da multi-sig wallet domin gujewa tara kudi mutum daya ya kwashe ba’asani ba. Kai a daidaikun mu da muke crypto zamu iya kirkirar multi-sig wallet muna ajiye dukiyarmu achikinta, sai mu bawa wasu amintattunmu kamar iyaye, ya’ya da sauransu (akalla mutane biyu, kai ka zama chikon na uku) yanda dole sai mutane biyu sun amince kafin ayi transaction. Hikimar hakan shine ko mutuwa mutum yayi, wayannan mutane biyun zasu iya chire dukiyar. Maimakon ace kudin sunki fita gaba daya saboda babu mai access da wallet din.
Anan zamuga cewa ba lallai sai mutum ya shiga crypto ba, ire-iren wayannan abunuwan zasu amfani mutane da yawa. Musamman yan kasuwa, kungiyoyi, da sauransu.
Sunusi Danjuma Ali
YouTuber II Founder, SCTv Africa