Update na karshe achikin shekarar 2024 akan Minings da Airdrops.
🌊 Wave wallet code na yau 👇
0uvim3
🔰 XENEA sun kammala campaign da ake amsa tambayoyi kullum domin amsar 100 GM. Sunce a saurari sabon update achikin sabuwar shekara ta 2025 idan Allah ya kaimu.
❄️ Akwai alamar Humanity Protocol suzo da tsari irin na Worldcoin, domin kuwa tuni suka fara raba na'urorinsu a wasu kasashen domin tantancewa. Saidai, na'urorin verification dinsu zanen dan yatsa suke dauka, wato fingerprint. Haka zalika, Humanity Protocol sun tabbatar da cewa RWT da akeyin mining shine zasuyi converting zuwa token dinsu mai suna $H. Don haka mu dage da claiming na RWT dinmu duk bayan awanni 24.
💎 Yau da misalin 12pm za'a rufe amsar discord role da minting na NFT a MIDAS YIELDER ga wayanda sukayi investing a platform dinsu. Don haka wayanda basuyi ba suyi kokari suyi kafi lokachi ya kure.
🦋
CEX.IO sunce snapshot na biyu zasuyi shine yana 5th January. A yanzu dai basu fadi tsayayyiyar rana ba, amma sunce zasu sanar idan loakchin yayi.
😥 Farashin OGC yayi raga-raga bayan kwana daya dayin launching dinsa. OGC ya fara da farashin $0.04, yayi da yawan mutane suka siyar da nasu akan $0.02. Yanzu haka farashin OGC ya ragargaje zuwa $0.0077. Har yanzu basu fadi ranar da zasu sakarwa mutane sauran OGC dinsu daya rage ba.
😃 Minings da Airdrops wayanda akesa ran zasu fashe a farkon shekarar 2025 (Q1) sun hada da HOT, CEX, XENEA, PIXEL, WAVE da TAPSWAP.
Wannan shine post dina na karshe achikin 2024, sai kuma idan Allah ya bamu tsawon rai zuwa 2025 In Sha Allah.