SCTv Africa HS


Гео и язык канала: Индия, Английский
Категория: Криптовалюты


Number one channel for verified news and updates on blockchain and cryptocurrencies.
Contact: sctvafrica@gmail.com
Youtube: youtube.com/@SunusiCryptoTV
X (twitter): x.com/SCTvAfrica
Facebook: https://www.facebook.com/sunusi.d.ali

Связанные каналы  |  Похожие каналы

Гео и язык канала
Индия, Английский
Категория
Криптовалюты
Статистика
Фильтр публикаций


Видео недоступно для предпросмотра
Смотреть в Telegram
Yanda ake bridging da staking achikin HOT wallet.

~ Ba lallai sai akan BSC network kadai zaku iya turo USDT dinku ba, zaku iya turowa akan wasu network din kamar TON network.

~ Idan akan BSC network ne, kuna bukatar BNB kadan domin biyan gas fee yayi bridging. Haka zalika idan akan TON network ne, kuna bukatar TON domin biyan gas fee. Kowanne zaku tura na $2 zaku dade kuna amfani dashi.

4.3k 1 15 13 91

✨ Amsar XENEA ta yau 👇🏽

Duk wanda kuka zaba daidai ne

✨ Wave wallet code na yau 👇🏽

0pxhut

Wayanda basu fara XENEA airdrop ba, subi wannan link dake kasa domin farawa👇🏽

https://t.me/Sunusicryptotv/2695

GM


Indan Kasan Ka Tara HOT....

🔥 Idan kasan ka tara HOT da yawa ina baka shawarar cewa ka dinga yin activities achikinsa domin gujewa fadawa matsalar rotten wood.

🔥 A yan kwanakin nan HOT suna sawa mutane rotten wood sosai, idan akayi musu magana sai suce accounts din bana mutane bane, bots ne suke mining din. Abu dayane kuma yake banbance accounts na bots da mutane shine ace ana activities a accounts din.

🔥 Activities kamar trading, bridging, staking, da sauransu sune suke banbance accounts na bot dana mutane. Don haka idan kanason account dinka ya tsira daga rotten wood, to dole kayi haqurin yin activities achikinsa. Trading zai iya sawa mutum ya samu riba ko asara, don haka mutum idan yana shakkar yin trading zaifi masa yana bridging da/ko staking domin kare HOT dinsa.

Misali, idan bridging mutum zaiyi saiya ware kamar $5 zuwa sama ta isheshi kullum yayi bridging sau daya ko biyu a rana har a gama mining din. Kuma $5 dinsa tana nan ba abinda zai sameta har a gama mining din.

Yanda zakuyi bridging din

~ Ku dauki wallet address dinku na TON achikin HOT, ku turo $ din akanta. Bayan yan mintuna zakuga $$ dinku achikin HOT account dinku. Sannan ku tura akalla 0.2 TON akan address din domin biyan gas fee aduk lokachin da zakuyi bridging.

~ Shikenan, kullum sai kuyi bridging wannan $$ din daga TON blockchain zuwa Near blockchain akalla sau biyuma yayi.

~ Wannan zai bawa HOT dinku kariya daga fadawa chakwakwikyar rotten wood.

🔥 Ku sani ni Sunusi Danjuma Ali banida alaqa ta kusa kota nesa da HOT team. Don haka ina baku wannan shawarar ne domin gudun kada su saka muku rotten wood kuce nayi musu magana akan su chire, ko kuma nayi musu rubutu a twitter. A mafi yawan lokachi hakan bai fiya tasiri ba, domin su project sun gama chin moriyar community alokachin.

🔥 Riga kafi tafi magani....

6.9k 1 7 29 129

✨ Amsar XENEA ta yau 👇🏽

Duk wanda kuka zaba daidai ne

✨ Wave wallet code na yau 👇🏽

0xmu8v

Wayanda basu fara XENEA airdrop ba, subi wannan link dake kasa domin farawa👇🏽

https://t.me/Sunusicryptotv/2695

GM


✨ Amsar XENEA ta yau 👇🏽

Duk wanda kuka zaba daidai ne

✨ Wave wallet code na yau 👇🏽

0kwr6l

Wayanda basu fara XENEA airdrop ba, subi wannan link dake kasa domin farawa👇🏽

https://t.me/Sunusicryptotv/2695

GM


✨️ Alhamdulillah. Nayi claiming $OVER dina, saidai naga sun kara mini yawansa, domin abaya 86 $OVER na samu amma yanzu naga ya koma 135 $OVER.

✨️ Sannan zaku iya dubawa ko sun baku na OKX Cryptopedia da mukayi. Nidai sun bani 9 $OVER. Ga link a kasa da zaku duba, kuma kuyi claiming idan kun samu.

https://cryptopedia.over.network/reward?

Kuyi pasting link din a discovery na OKX wallet dinku. Idan ya bude saiku duba.

✨️ Wayanda zasu sayarda nasu zasu iya turashi daya daga chikin kasuwannin da suka sanar zasuyi listing. Kamar BINGX, MEXC, Gate da sauransu.

8.6k 1 4 81 137

Dalilin Da Yasa Zan Rike $OVER

Aduk harkar kudi da nakeyi nafi damuwa da passive income akan active income. Passive income itace duk wata tabbatacciyar hanya da zata dinga kawo maka kudade kullum ko kuma a duk wani kayyadadden lokachi kamar duk sati ko duk wata, ba tareda kullum sai kayi wani aiki ba akansa. Active income kuma shine hanyar da zata dinga baka kudi masu nauyi amma kuma dole sai kayi wani aiki kafin kudin suzo.

Misali, ma’akachin albashi da kullum saiya fita aiki, amma yanada tabbachin a karshen wata za’a biyashi albashinsa. Wannan albashin active income, domin kuwa dole kullum sai yaje gurin aikinsa yayi aikin da aka daukeshi sannan ya chanchanchi samun albashi a karshen wata. Kenan idan ya mutu, koya ajiye aiki, ko kuma wata larura ta sameshi da zata hanashi yin aikinsa, wannan albashin nasa zai tsaya. To amma idan kuma ya tara kudin albashinsa, saiya gina gida ya bayar dashi haya, wannan gidan zai dinga kawo masa passive income. Ko mutuwa yayi, ko wata larura ta sameshi ya kwanta, za’a dinga biyansa kudin hayar gida ko kuma adinga biya iyalansa. Wannan shine banbanchin passive income da active income.

Da yawan masu kudi sunfi investing kudinsu akan abinda zai dinga kawo musu passive income. Misali, su zuba hannun jari a wani kamfani domin duk wata ana basu share dinsu na ribar da kamfani yake samu. Wannan share din ko mutuwa sukayi sai an dinga biyan iyalansu. Wannan duk misaline na rayuwarmu ta yau da gobe.

Idan muka dawo bangarenmu na crypto, akwai hanyoyi da yawa da suke bawa mutum passive income, wasu nayi bidiyonsu a shekarun baya. Wasu kudinka zaka zuba musu adinga baka shares kullum, yayin da wasu kuma aiki zakayi musu adinga biyanka fansho kullum har karshen rayuwarka data zurriyarka.

Inaso na rike $OVER bawai don kawai yanada potential ba, a’a saboda zai dinga bani passive income ne, shinema yasa nace zan siyeshi da yawa. Abaya nace inaso nayi running node na OVER Protocol, amma yanzu na chanja ra’ayin hakan saboda gaskiya harkokina bazasu barni na bashi lokachi ba, amma kuma zanyi palm-staking dinsa domin yana generating koda $0.5 ne arana as passive income, yayin da kuma yake kara daraja da yardar Allah.

Bari na fada muku wani sirrin crypto, duk project da yake da tsarin staking mai kyau, indai team dinsa da gaske suke sai kunga coin dinsu yayi daraja. Misali, baya-bayan nan akayi launching na Grass, sunzo da tsarin staking, wannan shine yasa token din yayi tashin da yayi kwanaki uku bayan launching. Saboda su turawa sun yarda da staking sosai amatsayin hanyar samun passive income, don haka suna iya zuba dubunnan daruruwan daloli domin su sayi coin suyi staking dinsa. Wayannan kudaden da suke hawa kan token sune suke kawo tashinsa kwanaki kadan bayan launching, kuma sune suke rike farashin token din domin basu saya domin suyi dumping daga ba. Don haka bayan potential na $OVER, wannan staking dinsa da shima wani abune da zaisa ya dinga daraja ahankali daga baya, musamman idan sunada tsarin APR/APY mai kyau.

…. Bayanin da yawa, don haka bari na tsagaita haka.

9.4k 1 7 38 322

✨ Amsar XENEA ta yau 👇🏽

2048

✨ Wave wallet code na yau 👇🏽

0phxaq

Wayanda basu fara XENEA airdrop ba, subi wannan link dake kasa domin farawa👇🏽

https://t.me/Sunusicryptotv/2695

GM


✨ Amsar XENEA ta yau 👇🏽

BIP-39

✨ Wave wallet code na yau 👇🏽

0xxoef

Wayanda basu fara XENEA airdrop ba, subi wannan link dake kasa domin farawa👇🏽

https://t.me/Sunusicryptotv/2695

GM


XENEA AMA code da akayi yau shine 👇🏽

XeneaDACS

Ku shigar dashi domin samun 2000 GEM

Wayanda basu fara NEXEA airdrop ba, subi wannan link dake kasa domin farawa👇🏽

https://t.me/Sunusicryptotv/2695


Genesis date
A blockchain, genesis date yana nufin ranar da blockchain fara aiki. Ma’ana, ranar da blockchain ya zama live, za’a iya kirkirar project akansa kamar kirkirar token, NFT, RWA, da sauransu. Alokachin da blockchain yake matakin testnet ba’a lissafashi amatsayin ya zama live, amma daga ranar da blockchain yabar matakin testnet zuwa mainnet, to wannan ranar itace genesis date dinsa.

Genesis block
Alokachin da blockchain yake a matakin mainnet, block na farko da aka kirkirar akansa akayi recording transaction achikinsa, ana kiransa da genesis block. Duk wasu blocks da za’a kirkira agaba akan wannan blockchain din zasu kasance sunada alaqa da wannan genesis block din. Haka zalika duk wani transaction da za’ayi recording akan blockchain din sai anyi linking dinsa da genesis block.

Genesis price
Idan har blockchain ya kasance coin dinsa shine project na farko da aka fara kirkira akansa, akan yiwa coin din farashi. Wannan farashin ana kiransa da genesis price. Bayan kirkirar coin na blockchain, akan siyarwa da wasu mutane na chikin gida coin din, kamar team, advisors, marketers, da sauransu. Ana sayar musune akan genesis price dukda cewa a mafi yawan lokachi akanyi vesting na coin din da aka siyar musu na wasu shekaru. Wannan genesis price din shine ake sanarwa duniya a farko kafin listing, kuma shine kasuwanni suke recording dinsa.

Misali, baya-bayan nan akayi launching na $XION, zamuga cewa genesis price dinsa ya fara da $0.2 adukkan kasuwannin crypto, amma a ranar saida farashinsa yakai $12. Haka $CORE genesis price dinsa ya fara sa $0.03 amma a ranar saida farashinsa yakai $7, hakama $APTOS ya fara da $1 amatsayin genesis price amma aranar sai daya buga $100….ire-iren hakan zaku gani akan dukkan wani coin na blockchain.

Ganin $0.1 genesis price na $OVER ba yana nufin cewa da wannan farashin zai tsaya ba. Balma zamu iya cewa mafi karanchin shine yayi X10 na genesis price dinsa. Ma’ana, mafi karanchi mu ganshi ya fara da $1 zuwa.

Allah ya datar damu da mafifichin alkhairansa

11.6k 1 12 19 194

✨ Amsar XENEA ta yau 👇🏽

Non-Custodial Wallet

✨ Wave wallet code na yau 👇🏽

0xk9n1

Wayanda basu fara NEXEA airdrop ba, subi wannan link dake kasa domin farawa👇🏽

https://t.me/Sunusicryptotv/2695

Karin Ilimi

Wallets sun rabu kashi biyu. Akwai custodial wallets da kuma non-custodial wallet.

✨ Non-Custodial Wallet ana kiransu da web3 wallets. Non-Custodial wallet sune idan za’a budesu ake bawa mutum kalmomi 12 ko 24 da ake kirasu da recovery phrase ko seed phrase. Wayannan kalmomin sune makullan wallet din mutum, idan ya chanja waya dasune zai iya dawo da wallet dinsa. Idan ya rasa recovery phrase dinsa ya rasa wallet dinsa har abada.

Non-Custodial wallet ba’a amfani da Gmail ko number waya yayin budeta, ba’ayi mata verification/KYC kafin ayi amfani da ita. Misalin non-custodial wallets sune Metamask, Trust wallet, OKX wallet, Phantom, da sauransu. Yanada kyau idan mutum ya bude non-custodial wallets ya rubuta recovery phrase dinsa a takarda domin adanawa.

Custodial wallets suna kamanceceniya sosai da centralize exchange. Custodial wallet basa bada recovery phrase, ana amfani da Gmail ne ko number waya yayin budeta, anayı mata KYC/verification. Misalin custodial wallet itace Remitano, Roqqu, Bundle, da sauransu.

Jumu’at Mubarak


Wave wallet suna building na gasken gaske.

Dazun nan suka saki wave trading bot na telegram. Kuma gaskiya yanada dadin aiki sosai, domin kuwa harna tura yar $11 domin gwada aiki dashi kamar yanda kuke gani.

Babban abin birgewa da wave trading bot shine yanada security check feature dazai taimaka maka wajen gane matsalar token. Saidai na binchikeshi sosai, security check feature dinsu bata tantance token mai matsalar honeypot, wanda shine babbar matsalar da tokens nakan SUI blockchain suke fuskanta daga devs dinsu. In Sha Allah zanyi rubutun jan hankalinsu a twitter domin su saka masa wannan feature din.

Yan kwanakin nafi yawan yin trading akan SUI blockchain, amma bana amfani da Dex Screener wajen neman token, domin abune mai wahala ka iya gane honeypot token. Kai tsaye nake shiga chikin wave wallet dina na nemi token da aka kirkira akanta nayi trading dashi.

Wave wallet sunyi tsari mai kyau tamkar na pump dot fun, ta yanda bazai yiwu mutum ya iya kirkirar honeypot token akanta ba. Don haka banida fargabar yin trading na tokens da aka kirkira akan wave wallet.

Kwana biyu banyi bidiyo ba sakamakon ina jarrabawa a makaranta, amma In Sha Allah a weekend din nan zan kammala. In Sha Allah zan dawo yin bidiyo, kuma zan fara da yanda zaku iya nemo token na trading akan wave wallet dama yanda ake trading akan wave wallet bot.

Wayanda suka iya amfani da trading bot, ga link na wave wallet bot a kasa 👇🏽

https://t.me/WaveTradingGlobalBot?start=GnNob3dfcGFpcl9yZWYOqtsKtpnMAg

12k 1 13 19 133

✨ Amsar XENEA ta yau 👇🏽

Yes

✨ Wave wallet code na yau 👇🏽

0lt48j

Wayanda basu fara NEXEA airdrop ba, subi wannan link dake kasa domin farawa👇🏽

https://t.me/Sunusicryptotv/2695

GM


Mara Wallet Sun Dawo Da Sabon Suna Mai Suna Jara. Ina Ake Ciki Da Maganar Kuɗin mu?

Da yawan ku kun san Mara, kuma an samu alkhairi duk da cewar a waccen lokacin akwai kuɗi da muke binsu da yawa da ba'a biya mu ba. Munyi magana da Ambassador ɗin su na Africa a inda yace mini gyara da sukeyi ne yasa muka daina jin ɗuriyar su. A halin yanzu sun chanza suna, sun chanza ma'aikatan da suka zo musu da matsala a baya, sannan sunyi blockchain ɗinsu, ƙari akan haka matsalar KYC da mutane suke ta samu ya saka sun yanke shawarar chanza tsarin su daga 'centralised system' zuwa decentralized system. Don haka yanzu bayan kayi register da Email, zasu sake baka seed phrase na wallet komai ya zama kaine kake da iko akansa.

Idan kayi MARA a baya, anaso ne ka buɗe Jara Wallet da wannan Email ɗin, saboda ta haka ne kaɗai zasu haɗa aikin ka na Mara da kayi a baya, da kuma wanda akeyi yanzu na Jara.

Ga yadda zakayi register da Jara:

✨ Ku tana link dake kasa. Idan ya bude muku, kuyi signup ta hanyar shigar da mail dinku tareda kirkirar password. Zasu tura muku da sako ta Mail dinku, a mafi yawan lokachi sakon nasu yana tsayawane a spam folder. Don haka saiku shiga spam folder dinku, sannan ku taba Looks Safe domin dawo da sakon zuwa primary folder dinku. Daga nan saiku tana CONFIRM SIGNUP.

https://app.getjara.xyz/join?refCode=629KSL71

✨ Ku dauko Jara wallet application a PlayStore ko AppStore, sannan kuyi Signin da bayanan da kukayi rijista.

✨ Daga nan saiku taba Create a new wallet. Zasu baku secret recovery phrase, ku tabbatar kun rubutashi kuma kun adanashi. Sannan zasu baku private keys, suma ku tabbatar kun adasu.

Shikenan! Kun kammala bude Jara wallet.

Yanda Zaku Tara Jara Points

💥 Daga chan kasan wallet dinku, akwai icons guda 4, na karshen mai tambarin Jara shine zaku shiga. A karkashinsa akwai abubuwa da yawa, kamar Games, Launchpad, Rapples da kuma Rewards.

💥 A karkashin na farkon wato Games, akwai LionTap. Idan kuka shiga zakuyi tapping dinsa na yan sakwanni, yana chika sai kuyi claiming na Jara Points dinku. Sai kuma bayan awanni biyu zaku kara dawowa kuyi tapping. Da hakane zaku tara Jara points.

Ubangiji Allah ya bamu sa'a.


Duk wani crypto project gatansa sune community dinsa. Duk kyawun use case na project da karfin utilities dake kan coin ko token dinsa, community sune gatansa ba use case ko utilities din ba. Kamar dai dan kasuwane, duk karfin jarinsa da kyawun kayan da yake sayarwa customers sune gatansa. Kamar kuma hakane duk ilimin influencer, community dinsa sune gatansa. Domin kuwa ita kanta kalmar influencer din indirectly tana magana akan community. Mutum zai iya zama mai ilimi, kuma iliminsa yana bashi kudi sosai, amma bashida influence. Zaku kara fahimtar hakane idan kuka kalli yanda manyan masu kudi suke dagewa da neman milki (koşu tsayawa yaransu) alokachin zabe, bawai kudin suke so su kara tarawa ba, a’a influence suke nema yanzu.

Duk wani project zaiso ace community dinsa mutanene da suka fito daga kowanne yanki na duniya, hakane zaisa ya zama global project. Amma Aduk da hakan kowanne project yanaso yaga ya karbu agurin yan Nijeriya saboda chikin kankanin lokachi zai hada babban community. Kowanne wani project da ake mining/farming/airdrop yan Arewa sunfi yan kowanne yanki a Nijeriya bada gudummawa saboda yawanmu da kuma dedication dinmu. Zaku yarda dani idan kuka duba cewa duk wani project da influencer na Arewa zai shiga sai kun ganshi a sawun gaba (top).

Dukda wannan gudummawar da muke bawa project, hakan baya bamu karfin fada aji akan duk project din da muka shiga, sannan a mafi yawan lokachi akarshe mune muke zama koma baya a wajen morar mafi yawan projects din. Hakan yanada alaqa da wasu matsaloli masu yawa daga Arewa crypto community (influencers da kuma community dinsu).

Wannan wani maudu’ine mai matukar muhimmanchi daya kamata mu tattauna domin maganin matsalolin. Saboda wasu dalilai, zan zabi nabar wannan maganar a yanzu, sai nan gaba na fito da matsalolin da kuma hanyar da zamubi domin gyarawa.

Wayanda basu fara NEXEA airdrop ba, subi wannan link dake kasa domin farawa👇🏽

https://t.me/Sunusicryptotv/2695


✨ Amsar XENEA ta yau 👇🏽

To Cache Data

✨ Wave wallet code na yau 👇🏽

0x5gvz

Wayanda basu fara NEXEA airdrop ba, subi wannan link dake kasa domin farawa👇🏽

https://t.me/Sunusicryptotv/2695

13k 1 5 20 73



$ORB yana $3.4M MC
$ORO yana $1M MC

Ba financial advice ba, amma indai kanada verified Worldcoin app, lallai ka duba yiwuwar sayensu ko kadanne.

They’re too early. Always DYOR


✨ Amsar XENEA ta yau itace kamar yanda muke gani ajikin hoton dake kasa.

✨ Code na wave wallet na yau shine 👇🏽

0ze6ej

Wayanda basu fara NEXEA airdrop ba, subi wannan link dake kasa 👇🏽

https://t.me/Sunusicryptotv/2695

Показано 20 последних публикаций.