Dalilin Da Yasa Zan Rike $OVER
Aduk harkar kudi da nakeyi nafi damuwa da passive income akan active income. Passive income itace duk wata tabbatacciyar hanya da zata dinga kawo maka kudade kullum ko kuma a duk wani kayyadadden lokachi kamar duk sati ko duk wata, ba tareda kullum sai kayi wani aiki ba akansa. Active income kuma shine hanyar da zata dinga baka kudi masu nauyi amma kuma dole sai kayi wani aiki kafin kudin suzo.
Misali, ma’akachin albashi da kullum saiya fita aiki, amma yanada tabbachin a karshen wata za’a biyashi albashinsa. Wannan albashin active income, domin kuwa dole kullum sai yaje gurin aikinsa yayi aikin da aka daukeshi sannan ya chanchanchi samun albashi a karshen wata. Kenan idan ya mutu, koya ajiye aiki, ko kuma wata larura ta sameshi da zata hanashi yin aikinsa, wannan albashin nasa zai tsaya. To amma idan kuma ya tara kudin albashinsa, saiya gina gida ya bayar dashi haya, wannan gidan zai dinga kawo masa passive income. Ko mutuwa yayi, ko wata larura ta sameshi ya kwanta, za’a dinga biyansa kudin hayar gida ko kuma adinga biya iyalansa. Wannan shine banbanchin passive income da active income.
Da yawan masu kudi sunfi investing kudinsu akan abinda zai dinga kawo musu passive income. Misali, su zuba hannun jari a wani kamfani domin duk wata ana basu share dinsu na ribar da kamfani yake samu. Wannan share din ko mutuwa sukayi sai an dinga biyan iyalansu. Wannan duk misaline na rayuwarmu ta yau da gobe.
Idan muka dawo bangarenmu na crypto, akwai hanyoyi da yawa da suke bawa mutum passive income, wasu nayi bidiyonsu a shekarun baya. Wasu kudinka zaka zuba musu adinga baka shares kullum, yayin da wasu kuma aiki zakayi musu adinga biyanka fansho kullum har karshen rayuwarka data zurriyarka.
Inaso na rike $OVER bawai don kawai yanada potential ba, a’a saboda zai dinga bani passive income ne, shinema yasa nace zan siyeshi da yawa. Abaya nace inaso nayi running node na OVER Protocol, amma yanzu na chanja ra’ayin hakan saboda gaskiya harkokina bazasu barni na bashi lokachi ba, amma kuma zanyi palm-staking dinsa domin yana generating koda $0.5 ne arana as passive income, yayin da kuma yake kara daraja da yardar Allah.
Bari na fada muku wani sirrin crypto, duk project da yake da tsarin staking mai kyau, indai team dinsa da gaske suke sai kunga coin dinsu yayi daraja. Misali, baya-bayan nan akayi launching na Grass, sunzo da tsarin staking, wannan shine yasa token din yayi tashin da yayi kwanaki uku bayan launching. Saboda su turawa sun yarda da staking sosai amatsayin hanyar samun passive income, don haka suna iya zuba dubunnan daruruwan daloli domin su sayi coin suyi staking dinsa. Wayannan kudaden da suke hawa kan token sune suke kawo tashinsa kwanaki kadan bayan launching, kuma sune suke rike farashin token din domin basu saya domin suyi dumping daga ba. Don haka bayan potential na $OVER, wannan staking dinsa da shima wani abune da zaisa ya dinga daraja ahankali daga baya, musamman idan sunada tsarin APR/APY mai kyau.
…. Bayanin da yawa, don haka bari na tsagaita haka.